Accessibility links

Mutanen Ireland Sun Amince Da Auren Jinsi Daya


Wasu masu marawa auren jinsi daya baya a kasar Ireland

A kasar Ireland ana shirin halalta auren jinsi guda bayan da kuri'ar raba gardamar da aka kada ta nuna cewa mafi yawan mutanen kasar sun amince da hakan.

Sakamakon farkoj na kuri’ar raba-gardama da aka kada a kasar Ireland, ya nuna cewa al’umar kasar, sun amince da a halalta auren jinsi daya.

Nan gaba a yau ne ake sa ran za a fitar da sakamakon karshe bayan da bayanai ke nuna cewa wadanda suka amince da auren na jinsi guda sun fi yawa.

Wannan dai shi ne karo na farko a duk fadin duniya da aka taba gudanar da irin wannan kuri’a kan auren jinsi daya a kasar da ke bin mazhabar Katolika.

Wannan matsaya da ‘yan kasar suka dauka, na zuwa ne shekaru kusan 20 bayan da aka cire luwadi a matsayin laifi.

Rahotanni na cewa dubban ‘yan kasar ta Ireland mazauna wasu kasashe, sun yi tattaki zuwa gida domin kada kuri’unsu.

Yanzu haka a nahiyar Turai, an halalta auren jinsi guda a fiye da kasashe goma, an kuma yi irin hakan ma a kasashen Brazil, da Argentina da Canada da New Zeland da Afrika ta Kudu da kuma wasu jihohin Amurka.

XS
SM
MD
LG