Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Kudu Maso Yammacin Jamhuriyar Dimukradiyar Congo Na Cikin Muguwar Yunwa


Mutanen da rikicin kasar ta Congo ta rabasu da muhallansu da MDD ke kokarin tallafa masu

Wani jami’in hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da garagdi kan halin da ake ciki a kudu maso yammacin Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, inda rikici ya jefa mutane miliyan 3.2 cikin kangin matsananciyar yunwa.

Cikin shekarar da ta gabata, rikici ya daidaita yankin Kasai na Congo inda mutane miliyan 1.4 suka fice daga gidajensu, rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu 3 tare da barnata bakin dayan kauyukan yankin, a cewar Claude Jibidar, jami’in da ke kula da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a Congo.

Ya kara da cewa yanayin da ake ciki a yankin za a iya kwatanta shi da abinda ke faruwa a Syria da Yamal.

Yanzu haka Congo wacce makekiyar kasa ce dake tsakiyar Afirka, tafi kowa ce kasa yawan mutanen da rikici ya tilastawa ficewa daga gidajensu a nahiyar Afirka.

Ba hukumar samar da abincin ce kadai take janyo hankula kan halin da ake ciki a kasar ta Congo ba, kungiyar likitoci ta kasa da kasa, wato Doctors Without Borderss a kwanan nan ta yi gargadi kan matsalar yunwa a tsakanin yara kanana, inda akan samu matsananciyar yunwa da ta kai kashi goma a wasu yankunan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG