Accessibility links

Mutanen Lamurde Sunce An Mayarda Su Saniyar Ware a Jihar Adamawa


Gwmnan jihar Adamawa Murtala Nyako

Al'ummar yankin Lamurde dake hijar Adamawa sun koka da irin wariyar da gwamnatin jihar ke nuna masu

Yayin wani taron manema labarai da shugabannin al'ummomin Lamurde suka kira sun koka da irin yadda jihar ta yi watsi da su.

Shugabannin yankin sunce an mayarda su saniyar ware a wurin gudanar da ayyukan cimma muradun karni da ake yi a jihar. Mr Polycap H Pari shugaban cigaban yankin Lamurde da kewaye yace harta dan asibitin da suke dashi an je an kware rufin da wawure kayan dake ciki da sunan za'a yi gyara. Yau fiye da shekaru biyu ke nan amma shiru a ke ji kamar an shuka dusa.

Mr. Pari ya kara da cewa abun da ya fi basu haushi shi ne sabon dakin da shugaban karamar hukumarsu Mr Solomon Obadiah ya gina wanda aka fara anfani da shi kimamnin wata shida sai aka zo aka cire jinkarsa. Da suka ce a fara da tsofofin gineginen da suka baci sai suka ki amma suka kwashe komi dake cikin sabon dakin suka tafi da shi. Yau shekara biyu ke nan komi ba'a yi ba. Asibitin ba shi da wutar lantarki. Idan mace zata haifu sai dai a yi anfani da tocila. Bugu da kari yakin na Lamurde bashi da wata hanya mai kyau. Idan akwai bukatar a dauki mara lafiya cikin gaggawa zuwa wani babban asibiti sai dai gyaran Allah.

Al'ummomin sun bukaci gwamnan jihar ya kafa kwamitin bincike a gano abun da aka yi da nasu kashi ashirin na duk ayyukan da yakamata a yi a yankin kamar yadda doka ta tanada. Tun da gwamnan yana iikirarin za'a yiwa kowa adalci a jihar to su al'ummomin yakin Lamurde suna bukatar ya yi masu adalci su gani a kasa.

Mai baiwa gwamnan jihar shawara ta fannin cin muradun karni Alhaji Ahmed Lawal yace al'ummomin da abun ya shafa su yi hakuri za'a bincika. Ya kuma shawarci mutanen karkara kada su bari wani dan kwangila ya taba kayan da aka kai masu. Ya yi kashedin kada wata al'umma ta bar dan kwangila ya taba kayan da aka kawo masu domin nasu ne. Laifin al'umma ne idan ta bari aka kwashe kayan da aka kawo masu.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG