Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Mubi Sun Koka Kan Yadda Harkokinsu Suka Tsaya Cik


Mutanen na Mubi su na kukar dokar hana fita da dare da aka kafa musu yayin da sabon kwamandan birged ta 23 ta sojojin Najeriya a Adamawa yake kama aiki

Mutanen garin Mubi a Jihar Adamawa, sun ce dokar hana fita daga karfe 7 na maraice har zuwa 6 na safe da aka kafa musu, tana kara jefa su cikin halin kunci da karyewar tattalin arzikinsu.

Yau kimanin watanni biyu ke nan da hukumomin tsaro suka kafa wannan dokar hana fita da dare, karkashin dokar-ta-bacin da aka ayyana a jihar ta Adamawa da kuma jihohin Borno da Yobe.

Mazauna garin na Mubi, wadanda suka yi ikirarin cewa akasarinsu 'yan kasuwa ne, sun fadawa Muryar Amurka cewa ko a bisa kuskure mutum ya kai karfe 7 na maraice a waje, yana fuskantar cin zarafi daga sojoji wadanda suke wulakanta mutane fiye da kima.

Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin kwamandan sojojin dake Mubi, Leftana-kanar Kayode Martin, amma bai amsa wayarsa ba.

A halin da ake ciki dai, sabon kwamandan birged ta 23 ta sojojin Najeriya dake Yola, Birgediya-Janar Rogers Nicolas, ya karbi ragamar wannan birged tare da yin kira ga jama'a da su ci gaba da ba su hadin kai, yana mai cewa an fara ganin amfanin matakan da aka dauka, kuma in jama'a suka kara hakuri, nan ba da jimawa ba za a dage dukkan matakan da suke takura musu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG