Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Ningi Sun Yi Zanga-Zangar Rashin Wutar Lantarki


Wani ma'aikacin hukuma yana gyara layin wutar lantarki

Mutanen garin Ningi sun ce watanni 6 ke nan ba su da wutar lantarki, amma hukumar wutar lantarki ta ce za a canja ta inda ake kai wuta garin a makon nan.

Mutanen garin Ningi a Jihar Bauchi sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadinsu da yadda aka shafe watanni 6 babu wutar lantarki a garin.

Akasarin wadanda suka yi wannan zanga-zangar sun ce wannan lamarin ya nakkasa ayyukan da suka dogara kan wutar lantarki, kamar masu aikin welda da sayar da kayayyakin sanyi na firij.

Mai martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, yace bai kamata a ce wannan lamarin ya gagari hukuma ba domin wadanda hakkin samar da wutar ke kansu ba su karfin ita hukuma ba.

Sai dai kuma manajan hukumar wutar lantarkin mai kula da garin Ningi, yace sun samu umurnin cewa su mayarda layin wutar dake zuwa Ningi ya koma daga Bauchi, fadar Jihar, maimakon daga garin Birnin Kudu na Jihar Jigawa inda ake dauko wutar yanzu. Yace tun lokacin da aka mayar da hanyar kai wuta zuwa garin na Ningi ta koma daga Jihar Jigawa, an yi ta fama da karancinta.

Wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad, ya ga wannan zanga-zanga, ya kuma aiko da rahoto kai daga Bauchi.

Mutanen Ningi A Jihar Bauchi Sun Yi Zanga-Zanga Kan Rashin Wutar Lantarki - 3:13
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG