Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Wani Kauye A Kamaru Na Hada Kudi Don Kallon Gasar Cin Kofin Duniya


Magoya Bayan Kamaru
Magoya Bayan Kamaru

A ranar Lahadi mai zuwa ne za a fara gasar cin kofin duniya ta maza a kasar Qatar, inda magoya baya a Afirka ke sha’awar kallon kungiyoyi biyar na nahiyar da za su fafata a gasar.

Tawagar kwallon kafa ta Kamaru, indomitable Lions, daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafar da su ka fi kwarjini, za su hadu da kungiyoyin kawllon kafa na Ghana, Morocco, Tunisia da kuma mai rike da kofin nahiyar Senegal.

Hatta kauyukan talakawa masu nisa da ba su da wutar lantarki suna hada kudi don sayen talabijin da samun wutar lantarki ta yadda su ma za su iya kallon gasar cin kofin duniya.

An jiyo karar injin janareta a Ouli da ke kusa da kan iyakan Kamaru da Najeriya, wanda kafin wannan watan ba su da wutar lantarki.

Kwamitin raya kauyen ya dauki hayar wani injiniya mai suna Dymbia Maurice dan shekaru 47 don ya saka musu injin samar da wutar lantarki.

Sai dai ya ce manufar ba ita ce samar wa kauyen wutar lantarki ba, za’a samar da wutar ne domin mazauna yankin su kalli wasannin kwallon kafa na gasar cin kofin duniya a Qatar ta talabijin.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG