Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 17 Sun Mutu Sanadiyyar Wani Harin Bom a Afghaistan


Harin Bom
Harin Bom

Wani harin bom na mota a babban birnin lardin Logarn a Afghanistan ya yi sanadiyyar kisan akalla mutum 17 wasu sama da 20 kuma suka jikkata, a cewar jami’an yankin.

Jami’an sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya auna wata tawagar jami’an tsaro a Pul-e-Alam babban birnin Lardin.

Mai Magana da yawun ‘yan kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya musanta cewa kungiyar ce ta kai harin, ya na mai cewa mayakan ba su da wata alaka da harin, wanda ya faru ‘yan sa’o’i kafin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma don bikin Babbar Sallah ta kwanaki 3 ta fara aiki.

A ranar Juma’a 31 ga watan Yuli aka fara bukukuwan Sallah kuma gwamnatin Afghanistan ta umurci jami’an tsaro su daina kai hari kan mayakan. Bayan Sallar Idi da aka yi ranar Juma’a, Shugaba Ashraf Ghani, a wani jawabi da ya yi ta talabijin ya sanar da cewa gwamnatinsa na shirin sakin sauran fursunonin ‘yan Taliban kusan 5,000 akan sakin jami’an tsaron Afghanistan 1,000 da mayakan suka yi, a karkashin yarjejeniyar musayar fursunoni da Amurka da ‘yan Taliban suka cimma.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG