Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum Fiye Da Miliyan Uku Ne Suka Kamu Da Coronavirus a Amurka


Yadda ake yi wa wata gwajin Coronavirus a Amurka
Yadda ake yi wa wata gwajin Coronavirus a Amurka

Adadin masu cutar Coronavirus a kasar Amurka ya zarta miliyan uku, yayin da akalla mutum 131,000 suka rasa rayukansu.

Hakan na zuwa ne dai-dai lokacin da babban kwararre kan cututtuka masu yaduwa a kasar ya yi gargadi ga Amurkawa kan cewa kar su kuskura su yi sakaci, saboda ganin raguwar yawan wadanda cutar ke kashewa.

Dr Anthony Fauci
Dr Anthony Fauci

Dr Anthony Fauci, shugaban cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar, ya yi wannan gargadin ne yayin wani zama na amsa tambayoyi da Sanata Doug Jones ta kafar Facebook.

“Ragon azanci ne a shiga murna don kawai adadin wadanda cutar ke kashewa ya ragu,” a cewar Fauci.

Ya kara da cewa, “akwai wasu abubuwa da dama masu hadarin gaske tattare da wannan cutar, kar mutum ya yi sake saboda tsammanin al’amarin ya yi sauki.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG