Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum Kusan Miliyan Uku Ne Suka Kamu Da Covid-19 a Amurka


Adadin wadan da suka mutu a sanadiyar annobar COVID-19 a Amurka ya kai dubu 130,000 a jiya litinin bisa ga kididdigar Jami’ar Johns Hopkins dake nan Amurka.

Ba a yawan mace mace sanadiyar coronavirus ba ne kawai Amurka take kan gaba a duniya, har da adadin wadanda suka kamu da cutar miliyan 2.9 da aka tabbatar.

A makon farko na watan Yuli da muke ciki kasar ta sanar da sababbin kamuwa dubu 50,000 a rana guda kamar yadda jihohin suka sanar a rana guda.

Wannan ya tabbatar da bayani na Masani akan cututtuka masu yaduwa, Anthony Fauci a jiya litinin cewa Amurka har yanzu tana cikin kangin annobar zagaye na farko iya wuya.

Daga cikin jihohin da cutar tafi tsananta akwai Texas dake kudu maso yammaci data sanar da sababbin kamuwa da COVID, mutum dubu 8,700 a rana guda. Asibitoci a jihar sun cika makil saboda karuwar masu coronavirus da ake kwantarwa. Abin ya fi tsananta a birnin San Antonio inda rudunar sojin kasar ke shawarar tura likitoci 50 su taimaka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG