Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutumin Da Trump Ya Zaba Sabon Atoni Janar Ya Ci Alwashin Kare Mueller


William Barr yana bayani gaban kwamitin shari'a a majalisa
William Barr yana bayani gaban kwamitin shari'a a majalisa

Mutumin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zaba don zaman sabon babban atoni janar na kasa, ya yi alkawarin kare mai bincike na musaman akan Rasha, daga matsin lamba na siyasa.

William Barr ya kuma bayyana cewa, zai kuma dauki mataki kan yadda Trump ke alakanta binciken da ake yiwa wasu na kusa da shi kan dangantakarsu da Rasha da cewa bita da kulli ne.

Da yake magana gaban kwamitin Shari’a na Majalisar Dokoki, Barr ya ce “Ban yi imanin cewa binciken da Robert Mueller ke gudanarwa bita da kulli bane” ya kuma kara da cewa shi zai bar binciken da ake ya ci gaba har karshe, kuma a fitar da sakamkon binciken ga jama’a da kuma Majalisa.

‘yan jam’iyyar Democrats dai sun dade suna nanata muhimmancin mai rike mukamin atoni Janal ya zamanto mai zaman kansa.

Barr, wanda ya yi aiki a matsayin atoni janar karkashin mulkin shugaba George H. W. Bush, ya fuskanci matsin lamba ne sabili da wata takarda da ya rubuta bara, yana kushewa Mueller domin bincike kan ko shugaba Trump ya yi kokarin shish-shigi a binciken da ake gudanarwa ta wajen korar shugaban hukumar binciken manyan laifuka -FBI James Comey a shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai .

A cikin takardar da ya rubuta wa mataimakin atoni janar Rod Rosenstein, wanda yake sa ido kan binciken da ake gudanarwa, dangane da katsalandan da ake zargin Rasha da aikatawa a zaben shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da goma sha shida, Barr ya bayyana cewa, bincike matakin da Trump ya dauka a kan Comey bai dace ba ko kadan.

Wannan batun takardar da ya rubuta watan Yuni bara, ya bayyana ne bayanda Trump ya zabi Barr dan shekaru 68, ya gaji Jeff Sessions, wanda Trump ya kora sabili da zame kansa da yayi daga binciken da ake gudanarwa kan rawar da Rasha ta taka a zabukan Amurka.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG