Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutuncin Yankin Ethiopia Na Cikin Hatsari


Amurka ta damu ainun game da barazanar da ake yi wa yankin Habasha. Babban mahimmanci a cikin waɗannan barazanar shine rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Tigray na ƙasar.

Mutane a Tigray na ci gaba da shan wahala mai tsanani na take hakkin ɗan adam kuma sama da miliyan ɗaya ba su da wadatar abinci. Haka kuma sojojin Habasha da na Eritiriya da ma wasu da ke ɗauke da makamai sun toshe taimakon agaji na gaggawa da ake buƙata.

"Amurka ta yi Allah wadai da kakkausan lafazi game da kashe-kashe, cin zarafin mata ta hanyar, da sauran take hakkokin bil'adama da dai sauran cin zarafin," in ji Sakataren Harkokin Wajen Antony Blinken a cikin wata sanarwa.

Haka kuma muna mamakin yadda aka lalata dukiyoyin fararen hula da suka hada da hanyoyin ruwa, asibitoci, da wuraren kiwon lafiya, da ke faruwa a Tigray. ” Amurka ta yi kira ga gwamnatin Habasha da ta hukunta wadanda ke da hannu a take hakkin bil adama, da kare fararen hula, da kuma tabbatar da kai kayan agaji ba tare da cikas ba.

Sakatare Blinken ya ce: "Duk da muhimmacin hulda da diflomasiyya, bangarorin da ke rikici a Tigray ba su dauki matakai masu ma'ana ba don kawo karshen tashin hankali ko neman sasanta rikicin siyasa cikin lumana."

Sakatare Blinken ya yi kira ga gwamnatin Eritrea da ta hanzarta dawo da dakarunta zuwa yankin na Eritrea da duniya ta amince da shi. Sai dai idan tashin hankali ya daina, yadda za a samu damar faɗaɗa ayyukan agaji, ƙarancin abinci na yanzu na iya haifar da yunwa.

Dangane da mawuyacin halin da ake ciki a cikin Habasha, Sakatare Blinken ya sanar da takaita bayar da biza ga duk wani jami'in gwamnatin Habasha ko na yanzu ko na da, ko jami'an tsaro, ko wasu mutane da suka hada da yankin Amhara da sojoji marasa tsari da membobin kungiyar People’s Liberation Front da ke da alhakin gurɓata sasanta rikicin na Tigray.

Waɗannan da suka ci zarafin mutane a cikin Tigray, da waɗanda suka hana a kai kayan agaji suma suna ƙarƙashin waɗannan ƙayyadewar. Dangin irin wadannan mutane suma na iya fuskantar wadannan ƙayyadewar.

Sakatare Blinken ya yi kira ga sauran gwamnatoci da su bi sahun Amurka wajen daukar wadannan matakan.

Bugu da kari, Kasar Amurka ta sanya iyaka a kan tallafin tattalin arziki da tsaro ga Habasha. Sakataren Blinken ya ce "Za mu ci gaba da ba da taimakon jin kai da kuma wasu muhimman kayan taimakon gaggawa ga Habasha." Za a ci gaba da aiwatar da takunkumin da ke nan kan taimakon ga Eritrea zai cigaba da zama.

Amurka ta himmatu wajen tallafawa kokarin sasanta rikicin na Tigray da kuma taimakawaal’ummar Habasha cimma sulhu da tattaunawa.

XS
SM
MD
LG