Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutune Miliyan 1 Suka Kamu Da Cutar COVID-19 a Los Angeles, Jihar California


An samu bullar sabon nau'in cutar COVID-19 na Birtaniya a Garin Los Angeles da ke jihar California a Amurka.

Ranar Lahadi 17 ga watan Janairu Jami’ar Johns Hopkins ta Amurka ta bada rahoton cewa mutun miliyan 94.5 ne suka kamu da cutar COVID-19 a fadin duniya. Amurka ce ke kan gaba da adadin mutun miliyan 23.7, daga nan sai India mai mutun miliyan 10.5, sai kuma Brazil mai miliyan 8.4.

Garin Los Angeles a jihar California shi ne ya zama gari na farko a tarihin garuruwan Amurka da ya sanar da samun mutun miliyan 1 da suka kamu da cutar COVID-19 ya zuwa yanzu. Rahoton yawan adadin ya kara zama da muni bayan da aka tabbatar da samun bullar sabon nau’in cutar ta coronavirus da aka gano a Birtaniya a garin.

Dr. Barbara Ferrer, daraktar hukumar lafiya ta garin, ta fada a wata sanarwa cewa, abin tashin hankali ne samun bullar sabon nau’in cutar a Los Angeles, yayin da cibiyoyin lafiyar garin suka cika makil inda yanzu haka ake da mutane sama da 7,500 da aka kwantar asibiti.

Kasar Norway, na gudanar da bincike kan wasu masu manyan shekaru fiye da 25 da suka mutu bayan da aka yi musu allurar riga kafin COVID-19 na kamfanin Pfizer. Cibiyar magungunan kasar ta ce mutanen da abin ya shafa da ma su na da wasu larurori.

XS
SM
MD
LG