Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutuwar Khashoggi: Wani Hoton Bidiyo Ya Bayyana


Jamal Khashoggi
Jamal Khashoggi

Hukumomin shari'a na Turkiyya sun dauki hoton wani bidiyo da ya nuna wani mutum mai kama da Jamal Khashoggi sanye da kayansa yana barin ofishin jakadancin Saudi Arabiya da ke Istanbul da ransa a ranar 2 ga watan Ocktoba.

Wani faifan bidiyo da ya bulla ya nuna wani wakilin gwamnatin Saudi Arabiya sanye da tufafin dan jaridar nan na Amurka mai suna Jamal Khashoggi, yana barin karamin ofishin jakadancin sa’udiyyar a ran 2 ga watan nan na Oktoba.

Hakan na nuna alamar cewa kamar an shirya wata hujjar cewa shi Khashoggi ya fita daga ofishin da ransa, don a boye cewa kashe shi aka yi.

Hukumomin shara’a na Turkiyya ne suka dauki hoton kuma suka nuna shi yau Litinin ga tashar telebijin ta CNN, inda ake ganin alamar cewa hukumomin sa’udiyya sun so su yi amfani da wani da ya yi kama da Kashoggi don boye gaskiyar abin da ya faru da shi.

Wannan bidiyon ya bulla ne a daidai lokacin da hukumomin Saudi Arabiya ke ba da wani sabon bayani, a kokarin da suke na fayyace gaskiyar abin da ya sami Khashoggi.

Khashoggi marubuci ne mai yawan sukar lamirin Yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman da kuma rawar da kasar ke takawa a yakin Yemen, a rubuce-rubucen da yake yi a jaridar Washington Post.

A halin yanzu kuma, kasar Saudi Arabiya ta ce a yau Litinin Yarima Mohammed Bin Salam ya yi magana ta waya da iyalan dan jaridar domin yi masu ta’aziya akan kisan dan jaridar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG