Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutuwar Yara Kanana Ta Ragu


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar cewa mutuwar yara kanana masu shekaru kasa da biyar ta ragu

Wani sabon rahoto ya nuna cewa,an sami raguwar mutuwar kanananan yara kasa da shekaru biyar da kimanin rabi tun daga shekara ta dubu da dari tara da casa’in lokacin da aka kafa muradun karni.

Duk da gagarumin ci gaban da aka samu, Majalisar Dinkin Duniya tace yana yiwuwa kasashe da dama su kasa cimma burin shawo kan matsalar da kimanin sulusi.

A shekara ta dubu da dari tara da casa’in, kananan yara miliyan goma sha biyu da dubu dari bakwai ‘yan kasa da shekaru biyar suka mutu, galibi sakamakon kamuwa da cututukan da ake iya magancewa. Bisa ga rahoton Majalisar Dinkin Duniya, fiye da kanannan yara miliyan shida suka mutu kawo yanzu. Duk da yake an sami ci gaba ainun, kwararru a fannin lafiya sunce ana bukatar kara dage damtse domin ceton rayukan kananan yara dubu goma sha shida da suke mutuwa kowacce rana.

Rahoton ya nuna cewa, galibin kananan yara suna fuskantar barazana ne a watan farko da haihuwarsu, lokacinda kashi 45 cikin dari na kanannan yara kimanin miliyan biyu suke mutuwa a makon farko na haihuwarsu.

Rahoton yace kimanin kasashe sittin da biyu sun cimma burin muradun karni na rage adadin kanannan yaran dake mutuwa da sulusi. Yayinda kasashe 74 kuma suka rage yawan kananan yaran dake mutuwa da kimanin rabi. Rahoton yace cututakan da suke katse hanzarin kananan yara sun hada da ciwon hakarkari, matsala a lokacin haihuwa, da ya hada da haihuwar bakwanni, gudawa, da kuma zazzabin ciwon sauro.

XS
SM
MD
LG