Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Gargadi Putin Kan Kutse - Obama


Shugaban Rasha Vladimir Putin (Hagu) da takwaran aikinsa na Amurka Barack Obama (Dama) a lokacin wani taro a China a watan Satumba

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce, ya fito karara ya fadawa takwaran aikinsa na Rasha Vladmir Putin da ya dakatar da  kutsen da Rashan ke yi akan Amurka, ko kuma Rashan za ta dandana kudarta.

Shugaba Obama dai bai yi wata-wata ba wajen bayyana wanda ya ba da umurnin a yi kutse a akwatin aike sako na email din Jam’iyar Democrat.

A lokacin ganiyar yakin neman zaben shugaban Amurka ne aka zargi ta yi kutse, zaben da ya yi matukar zafi tsakanin Hillary Clinton da Donald Trump.

“Gani na yi cewa, hanya mafi dacewa wajen ganin hakan bai sake faruwa ba shi ne na yi mai magana kai tsaye, na kuma fada mai cewa ya daina, idan ba haka ba, ya kiyayi abin da zai biyo baya.” In ji Obama.

Shugaban ya yi wadannan kalamai ne yayin da ya ke taron manema labaransa na karshe a wannan shekara.

Sai dai Obama bai fayyace ko wadanne irin matakai Amurka za ta dauka ba idan har Rasha ta sake yi mata kutse.

Obama har ila yau ya dora alhakin halin da Syria ke ciki a yau akan Rasha, yana mai cewa wahalar yunwa da yakin da birnin Aleppo ke fama da shi, gwamnatin Bashar – al Assad da Rasha ne suka janyo.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG