Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nada Robert Mugabe Jakadan Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya Ya Jawo Cece-Kuce.


Tedros Adhanom Ghebreyesus. Darektan hukumar kiwon lafiya ta MDD.
Tedros Adhanom Ghebreyesus. Darektan hukumar kiwon lafiya ta MDD.

Darektan hukumar Tedros Ghebreyus, dan Afirka na farko da zai jagoranci hukumar ne yayi wannan nadin.

A wani mataki da ya janyo cece-kuce, hukumar kiwon lafiya ta duniya ta nada shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya zama "jakadanta na musamman" domin ya taimaka wajen kara jawo hankali kan cututtuka da basa yaduwa, kamar bugun zuciya, da shanyewar wani bangare ko jiki ko gaba, da tarin asthama.

Darektan hukumar kiwon lafiyan Tedros Adhanom Ghebreyesus, dan Afirka na farko da zai jagoranci hukumar, nan da nan ya sami suka daga kungiyoyin rajin kare hakkin Bil'Adama da ma wadansu kan wannan nadin.

Hillel Neuer, babban darektan wata kungiya raji mai cibiya a birnin Geneva, da ake kira UN Watch, ya fada cikin sanarwa da ya bayar cewa "gwamnatin Robert Mugabe ta gallazawa masu rajin kare hakkin BIl'adama, ya murkushe masu rajin kare demokuradiyya, ya maida kasar da zata iya samar da abinci ga nahiyar Afirka baki daya zuwa halin-ni-'yasu."

Neuer, ya kara da cewa wai yau "MDD ta tallata wannan kasa a zaman mai goyon bayan kiwon lafiya, abun takaici ne."

"Shawarar nada Robert Mugabe a zaman "jakadan hukumar kiwon lafiya na musamman abun damuwa ne kuma bai dai-dai bane," in ji Dr. Jeremy Farrar, darektan wata kungiyar agaji a Britaniya da ake kira Wellcome Trust. "Robert Mugabe ya gaza ako wani rukuni kan manufofin hukumar kiwon lafiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG