Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce yankin nahiyar turai ya wuce China a matsayin yankin da cutar coronavirus ta fi addaba a duniya.
A jiya Juma’a shugaban hukumar Tedros Ghebereyesus ya fadawa manema labarai a birnin Geneva cewa, ana ci gaba da samun karin wadanda ke kamuwa da cutar a kullum sama da abin da aka gani a China a lokacin da cutar ta tashen bazuwa.
Kasar Italiya ta bayyana a jiya Juma’ar cewa, adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu da mutum dubu 2,500 cikin sa’o’i 24 da suka gabata, abin da ya kai jimillar masu dauke da cutar a kasar zuwa 17,660.
Duk da cewa, Burtaniya ba ta cikin kasashen da Shugaba Trump ya haramtawa shiga Amurka, akwai daruruwan mutane da suka kamu da cutar a kasar da ma Ireland.
Hakan ya sa Firai Minista Boris Johnson ya fito baro-baro ya fadawa al'umar kasar gaskiya.
“Ya zama dole na fadawa al’umar Burtaniya gaskiya, iyalai da dama za su rasa masoyansu tun kafin wa’adinsu ya yi.” In ji Johnson.