Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nahiyar Turai Ta Zama Dandalin Coronavirus


Shugabar Kungiyar Tarayyar turai, Ursula Von Der Leyen

Nahiyar turai ta zama wurin da Cutar COVID -19 ta fi barna, yayin da kasar nahiyar Turai da cutar ta fi shafa, wato Italiya, ta bayyana cewa daruruwan mutane sun mutu jiya Lahadi.

Adadin mutane da suka mutu a kasar ta Italiya a yanzu sun zarta 5,400.

Dukkan ayyukan da ba na bukatar yau da kullun ba, an rurrufe a kasar, a kokarin ta na dakile annobar ta Coronavirus.

"Wannan ne mafi mawuyacin yanayi da mu ka shiga, tun bayan yakin duniya," in ji Firai ministan kasar, Giuseppe Conte.

Cibiyar nazari kan cutar coronavirus ta Jami’ar John Hopkins, ta ce akwai a kalla mutum 53, 578 wadanda aka tabbatar sun kamu da kwayar cutar a Italiya.

Kasar Cuba ta tura likitoci da jami'an jinya zuwa kasar ta Italiya, domin kai dauki wajen magance cutar.

Kungiyar Tarayyar Turai EU, ta tabbatar wa kasar ta Italiya cewa bashin da ake bin ta ba zai hana ta ranto kudi don magance cutar ba.

Shugabar kungiyar ta EU Ursula Von Der Leyen ta ce ba za a kyale ’yan kungiyar su tunkari wannan matsalar su kadai ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG