Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Abba Kyari Ya Rasu


Abba Kyari
Abba Kyari

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya, Mallam Abba Kyari ya rasu.

Kakakin Shugaba Muhammadu Buhari Femi Adesina ne ya bayyyana hakan a wata sanarwa da ya fitar wacce VOA ta samu.

“Muna masu cike da alhinin sanar da cewa, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Mallam Abba Kyari ya rasu.” Sanarwar ta nuna.

Ta kuma kara da cewa, “an samu marigayin da cutar COVID-19, kuma ya yi ta karbar magani. Amma ya rasu ranar Juma’a 17 ga watan Afrilun 2020. Allah ya jikan sa.”

Nan gaba za a sanar da shirye-shriyen jana’izarsa, a cewar sanarwar.

A karshen watan Maris aka yi wa marigayin gwajin cutar aka kuma gano cewa yana dauke da ita.

Gabanin hakan, Kyari, ya yi tafiya zuwa Jamus wacce take fama da cutar a lokacin inda ya je halartar wani taro a farkon watan Maris.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG