Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Adadin Masu Coronavirus Ya Doshi 100


Wani Mutum sanye da rigar kariya a yankin Wuhan kasar China a ranar 28 ga watan Maris 2020. REUTERS/Aly Song

Hukumar kare yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya, ta ce adadin wadanda annobar coronavirus ta kama ya cilla zuwa 97.

Sabbin alkaluma sun nuna cewa, an samu karin mutum 8 a ranar Asabar 28 ga watan Maris.

"Da misalin karfe 10:40 na dare ranar 28 ga watan Maris, Najeriya na da mutum 97 da suka kamu da cutar #COVID19, sannan mutum daya ne ya rasu."

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo da na Twitter inda ta ce, daga cikin sabbin mutum 8 da aka gano, 2 a Abuja suke, 4 a Oyo, 1 a Kaduna sannan 1 a Osun.

Bayanan da hukumar ta kara fitarwa sun jaddada cewa, har yanzu mutum daya ne ya mutu sanadiyyar cutar a baki dayan kasar.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG