Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya da ake kira NCDC a takaice ta sanar da cewa an samu karin mutum 229 da suka kamu da cutar COVID-19.
Gaba dayan adadin wadanda suka kamu da cutar yanzu ya kai 8,068 a kasar.
Jihar Legas da ke kan gaba a wajen yawan masu kamuwa da cutar ta samu karin mutum 90 da suka kamu da cutar ta coronavirus, a cewar sanarwar da NCDC ta fitar a shafinta na Twitter.
Sauran jihohin da aka samu karin masu cutar sun hada da Katsina inda aka samu mutum 27, 26 a Imo, 23 a Kano,14 a babban birnin tarayya Abuja, 12 a Filato,
Sauren jihohin sun hada da Ogun mai mutum 9, 7 a Delta, 5 a Borno, 5 a Rivers, 4 a Oyo, 3 a Gombe, 2 Osun, 1 a Anambra, 1 a Bayelsa.
Ya zuwa daren ranar Litinin 25 ga watan Mayu, mutum 2,311 suka warke daga cutar, yayin da wasu su 233 suka mutu.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 24, 2021
Adadin Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 Ya Haura 120,600 a Najeriya
-
Janairu 24, 2021
Gwamnan Jihar Oyo Ya Ce Ba Sa Adawa Da Fulani Makiyaya
-
Janairu 23, 2021
Rikicin Cikin Gida Ya Kunno Kai a Jami'yyar APC Mai Mulki - Dalung
-
Janairu 22, 2021
Wasu 'Yan Arewa Sun Ce Wa Buhari: Mun Gaji Da Gafara Sa.
-
Janairu 22, 2021
An Mayar Da Wutar Gidan Shagari Da Aka Yanke
-
Janairu 19, 2021
Za A Baiwa 'Yan Kasashen Waje Lambar Zama Najeriya Ta Wucin Gadi
Facebook Forum