Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Adadin Wadanda Suka Kamu Da Cutar Coronavirus Ya Kai 51


A wani sabon rahoto da cibiyar dake lura da dakile cututtuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC ta fitar, ta ce an samu karin majiyyata biyu daga Abuja, biyu daga Legas, sai kuma guda daya daga jihar Rivers da suka kamu da cutar coronavirus, abinda ya sa adadin ya kai 51 yanzu.

A yau ne dai aka fara amfani da dokar rufe kasuwanni a birnin Legas. A jawabinsa ga al’umar jihar, gwamna Babajide Sanwo-olu, ya ce shagunan saida abinci da na magunguna ne kawai za a daga wa kafa, bisa la’akari da muhimmancinsu a yanayin da ake ciki.

Alhaji Umar Atina, wani mai shagon saida abinci ne a birnin Legas, ya ce gaskiya matakan da gwamnati ta dauka basu shafe su ba, sai dai kuma suna kiyaye matakan ne domin guje wa kamuwa da wannan cuta.

Shi kuma Alhaji Awaisu Giwa Kuta, cewa yayi ana daukar alhakin talaka ne kawai, domin wannan cuta ce da masu hali suka dauko amma yanzu ana sanya wa talaka takunkumin da zai hana shi neman abinci. Ya kamata gwamnati ta sake duba wadannan dokoki a cewarsa.

Yanzu haka dai ganin yadda shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, Abba Kyari da gwamnan jihar Bauchi suka kamu da cutar, shugaban gwamnonin Najeriya ya umarci gwamnoni ‘yan uwansa su kai kansu asibiti kuma su killace kansu. Tuni wasu gwamnonin da suka hada da na Niger, Nasarawa, Ekiti da Edo suka killace kansu suka kuma fara neman shawarwarin likitoci.

Saurari Karin bayani cikin Sauti.

Najeriya: Adadin Wadanda Suka Kamu Da Cutar Coronavirus Ya Kai 51

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG