Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: An Kalubalanci Kudaden Da 'Yan Majalisa Za Su Kashe Wajen Sayen Motoci


taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade
taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

Kungiyoyin Yaki da Cin hanci da rashawa da kuma kare hakkin dan Adam, irin su SERAP da EIE da kuma wasu ‘yan kishin kasa su 6,721 ne, suka amince da su shigar da kara akan yadda ‘yan Majalisar dokoki a Najeriya, da za su kashe kudi har Naira biliyan 5 da rabi, wajen sayan motocin hawa.

Kungiyoyin sun ce, sun shigar da kara ne akan cewar, suna so a haramta wa Majalisar kashe wadannan Kudade, saboda ya sabawa kashi 57 cikin kashi na 4 na tsarin sayen kayan amfani na shugabanin Majalisar Dokokin kasa, da aka kirkira a Kundin Tsarin Mulkin Majalisar, a shekara 2007.

Kungiyoyin sun ce ya zama wajibi Majalisar ta zabge yawan adadin kudaden da suke so su sayi motocin da su.

Daya cikin 'ya'yan Kungiyoyin Salihu Dantata Mahmud, ya ce, ba zai yiwu suna ganin talauci da yunwa, da rashin biyan kudaden makarantan yara, da rashin magunguna, sannan su yi shiru ba, domin ai an zabe su ne domin su yi dokoki da za su canja rayuwar al'umma ba kashe kudadede barkatai ba.

Shima Komred Bako Abdul, wanda ya wakilci kungiyar CAMPAIGN FOR DEMOCRACY a lokacin shigar da karar ya ce, almubazaranci ne barin ‘yan Majalisar su sayi motoci na yawan wadannan kudade. Ya ce, ‘yan Majalisar su yi maza-maza su janye wanan kuduri na sayen motoci domin su wakilan mutane ne ba wakilan kansu ba ne.

Barista Mainasara Ibrahim Umar ya yi karin haske akan abinda doka ta tanada game da irin wannan mataki na kashe makudan kudade duk shekaru hudu inda yake cewa, babu wata doka da ta tanadi kashe irin wadannan kudade, hasali ma su ‘yan Majalisar ne suka yi dokoki iri daban daban domin kare dukiyar al'umma, amma kuma su ne suke kokarin karya dokokin.

Ga rohoton Wakiliyar muryar Amurka, Medina Dauda, Daga Abuja Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG