Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: An Kama Masu Safarar Jarirai a Jos


Jarirai

Rundunar tsaro ta musamman a jihar Filato ta gano wani wurin da ake sayar da jarirai a cikin birnin Jos.

A yayin da yake zantawa da manema labarai kwamandan rundar tsaro ta Special Task Force (STF) a jihar Filato, Manjo Janal Nicolas Rogers, yace sun kama wasu mutane da suka da hada da maza takwas da mata uku, wadanda ake zargi da sayar da jarirai da kuma safararsu zuwa Legas da Abuja da Lokoja.

Kwamandan yace sun kame mazan ne da suke zarginsu da yiwa ‘yan matan ciki bayan da akayi hayarsu su aikata hakan.

‘Daya daga cikin ‘yan matan da aka kama mai suna Happiness John, wadda tace ba ta yarda da ta sayar da yaron ta ba, wanda hakan yasa ta kai rahoto gurin jami’an tsaro. Happiness, tace “Sanda ina da ciki kawata tace tunda ina da ciki nazo zasu kama min ‘daki inna haihu zasu kai yaron suje su sayar, don sun saba sayarwa tana zuwa Abuja ta sayar da nata.”

Ta ci gaba da cewa kawartata ta gaiyaceta zuwa Lafiya, don ta nuna mata inda za a sayar kuma zasu bata jari. Inda kuma suka dauke ta suka bata wasu magunguna domin ta haihu.

‘Yammatan dai sun bayyana cewa wadanda ke sayan jariran na su sukan kama musu ‘daki ne su ajiyesu har sai sun haihu, su basu kudi kalilan su kuma tafi da jariran na su.

Rundunar tsaro ta STF dai tace za ta ci gaba da gudanar da bincike har sai ta gano wadanda ke sayan jariran da kuma inda ma suke kaisu.

Domin karin bayani ga rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:45 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG