Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAJERIYA: An Sami Mutum Na Farko Da Ya Rasu Sakamakon Coronavirus


Coronavirus Updates

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta najeriya, NCDC ce ta sanar da rasuwar sa a shafinta na twitter.

Marigayin, tsohon shugaban hukumar kayyade farashin man fetur ta Najeriyar Suleiman Achimugu, ya rasu ne makwanni biyu bayan komawar sa Najeriya daga kasar Britaniya inda ya je jinya.

Iyalansa sun bayyana cewa, ya fara nuna alamun cutar ne ranar Talata da ta gabata, bayan an gudanar da gwaji kuma aka tabbatar yana dauke da wannan cutar, aka dauke shi zuwa asibitin kwararru na Gwagwalada a Abuja inda aka ci gaba da jinyar sa har zuwa asubahin yau da ya cika.

Tuni hukumar yaki da cutuka ta kasar ta dauki dawainiyar jana’izarsa, tare kuma da killace iyalansa a gidansu har zuwa wani lokaci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG