Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: An Samu Karin Mutum 13 Masu COVID-19


Wasu ma'aikatan lafiya suna hutawa a South Jakarta da ke Indonesia (Hoto: Antara/Asprilla Dwi Adha via Reuters)
Wasu ma'aikatan lafiya suna hutawa a South Jakarta da ke Indonesia (Hoto: Antara/Asprilla Dwi Adha via Reuters)

Hukumar kare yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta ce an samu karin mutum 13 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar.

Hakan na nufin adadin masu dauke da COVID-19 a Najeriya wacce ta fi kowacce kasa yawan al’uma a nahiyar Afirka ya kai 318.

“A ranar 11 ga watan Afrilu, an samu sabbin masu dauke da cutar COVID-19 13 a Najeriya.” NCDC ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

“Ya zuwa yanzu, ana da tabbacin mutum 318 ke dauke da cutar, an sallami mutum 70 kana 10 sun mutu.”

Cikin mutum 13 da aka gano, "11 a Legas suke, daya a Delta, daya a Kano,” kamar yadda shafin yanar gizon na NCDC ya nuna.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG