Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Ana Neman Wadanda Suka Yi Cudanya Da Masu Coronavirus


Nan wani soja ne yake gwada zafin jikin wani mutum da ya kai ziyara asibitin soji da ke Yaba a jihar Legas
Nan wani soja ne yake gwada zafin jikin wani mutum da ya kai ziyara asibitin soji da ke Yaba a jihar Legas

Cibiyar da ke kula da ayyukan gaggawa ta EOC a Najeriya, ta ce tana aiki tare da gwamnatin jihar Legas domin gano mutanen da suka yi cudanya da sabbin mutum hudu da aka samu da cutar coronavirus a jihar.

Hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka ta NCDC ce ta bayyana hakan a shafinta na yanar gizo a bayanan da ta sabunta kan cutar ta coronavirus a baya-bayan nan.

A ranar Alhamis, hukumar ta tabbatar da samun karin mutum hudu da ke dauke da cutar wacce ake wa lakabi da COVID-19.

Daga cikin mutanen, akwai wanda ya dawo daga Burtaniya, sannan akwai wanda ya koma Najeriya daga Faransa.

Mutum na uku kuma ya yi cudanya ne da daya cikin wadanda aka samu da cutar yayin da na hudun kuma ba shi da wasu bayanai da suka nuna ya yi wata tafiya.

Shekarun mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar sun kama ne daga 23 zuwa 59, sannan biyu mata ne biyu kuma maza.

Yanzu Najeriya na da adadin mutum 12 kenan da aka samu da cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG