Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ba Ta Amince Da Rage Darajarta Da Kamfanin Moody’s Ya Yi Ba - Ministan Kudi


Zainab Ministan Kudin Najeriya
Zainab Ministan Kudin Najeriya

 Ministar kudin Najeriya ta ce a ranar Alhamis din nan ba ta amince da, abin da ta kira, wani abin mamaki, da hukumar Moody’s ta yi na rage darajar kasar game da basussuka ba, tana mai cewa tuni gwamnatin kasar ta magance matsalolin da hukumar ta bayyana.

WASHINGTON, D.C. - Kamfanin Moody's ya rage darajar kasar mai arzikin man fetur a yammacin Afirka a makon da ya gabata zuwa Caa1 daga B3, yana mai cewa ana ganin tsarin kasafin kudi da bashi na gwamnati zai ci gaba da tabarbarewa, sanarwar da ta sa darajar alakar dala da kudin Najeriya ke tabarbarewa.

“Rage darajar Najeriya din da Moody's ya yi, ya zo mana da mamaki domin mun gabatar da dukkan ayyukan da muke yi na tabbatar da tattalin arziki,” in ji minista, ga manema labarai a Abuja.

"Amma waɗannan hukumomi ne na waje waɗanda ba su da cikakkiyar fahimtar abubuwan da ke faruwa a cikin gida."

Ta ce tana tsammanin awon S&P, wanda za a fitar ranar Juma'a, zai fi inganci.

"Awon S&P ba daidai yake da na Moody's ba. Sun fito da ingantaccen tsarin kimanta awo," in ji ta.

Najeriya dai ta fuskanci karancin man fetur sakamakon satar danyen mai a shekarun baya-bayan nan, duk da cewa man da ake hakowa ya fara karuwa kamar na da.

Haka kuma ta sha fama da karancin dala tare da yawan basussuka wanda ya ke lashe kudaden gwamnati.

Moody's dai ya kawo waɗannan abubuwan ne a matsayin dalilan da suka kawo faduwar darajar.

-Reuters

XS
SM
MD
LG