Accessibility links

Yayin da yake zantawa da wakilin Muryar Amurka a Legas gwamnan jihar Neja ya tabo batun rikicin jam'iyyarsu da rashin shugabancin nagari a kasar.

A cikin zantawarsa da wakilin Muryar Amurka a Legas Dr Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja ya tabo wasu batutuwa har da na rashin shugabanci na gari.

Dangane da rikicin da ya barke a jam'iyyarsu ta PDP gwamna Babangida Aliyu ya ce wannan ba sabon abu ba ne a faggen siyasa. Ya ce duk abun da suke kurari a kai shi ne a yi adalci domin hana wakilan Adamawa shiga babban taro jam'iyyar ba da wata kwakwarar hujja ba, ba adalci ba ne. Da aka gaya masa cewa baya ganin abun da suke yi ka iya rusa jam'iyyarsu sai ya ce yana ganin masu fadan hakan mutane ne da basu san siyasa ba. Ya ce abubuwan da suka faru a Adamawa, Rivers da Sokoto su suka kawo maganganu. Ya ce cewa aka yi a gyara kuma gyara kayanka ai ba sauke mu raba ba ne. Ya ce cewa muka yi a dubi wadannan abubuwa domin a gyara tafiya.

Dangane da kalamun Bamanga Tukur sai ya ce yana da 'yancin ya fadin albarkacin bakinsa kuma yana da tashi irin basirar. Watakila kuma ya mayarda lamarin abun da ya shafeshi shi kadai. Gwamnan ya kuma karyata cewa su basu ce a sake shugaban jam'iyyarsu ba ko kuma suna neman hana shugaba Jonathan sake tsayawa takara.

Makasudin kai gwamnan Legas shi ne bada lacca mai take hadewar Najeriya daga 1914 kawo yanzu, alfanu ko rashin alfanunsa. Da aka tambayeshi ya duba inda Najeriya ta fito da inda take yau da kuma inda ta nufa shin kwalliya ta biya kudin sabulu. Ya ce idan aka duba abubuwa sai a godewa Allah amma kodayaushe ana bukatar gyara. Kodayake kasar ta fara tafiya mai nisa sai a gode amma kasar tana fama da rashin shugabanni nagari. Da a ce an cigaba da yadda shugabannin farko suka gudanar da kasar da can da ba haka zamu kasance ba. Wahaloli da basu yi mana katutu ba kamar yadda suke yanzu.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.

XS
SM
MD
LG