Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAJERIYA: Buhari Ya Waiwaya Ayyukan Gwamnatocin Baya da Suka Gaza Aiwatarwa


Shugaba Muhammad Buhari

Yayinda gwamnatin Buhari ta dukufa da yaki da ta'adanci da cin hanci da rashawa wasu na ganin kamata yayi ta waiwayi ayyukan ci gaban kasa da gwamnatocin baya suka tsara zasu yi amma basu aiwatar ba.

Wasu 'yan Najeriya na ganin kamata yayi gwamnatin Buhari tayi waiwaye akan mahimman ayyukan cigaban kasa da tsoffin gwamnatocin da suka gabata suka kirkiro amma basu aiwatar ba.

Tsarin da shugaba Musa Yar'Adua ya yi da wanda Goodluck Jonathan ya tsara na cikin cigaban kasa ne. To saidai daga bisani babu labarinsu bayan shugabannin tsoffin gwamnatocin. Wasu na ganin koma baya ne ga kasar.

Malam Abubakar Sahabi yace kamata yayi a samar da doka da zata tilasta cigaban ayyukan tsohuwar gwamnati da ta gabata muddin na cigaban kasa ne.

Majalisun tarayyar Najeriya su kafa doka idan wani ya gaji gwamnati ya tarad da ayyukan da aka soma na cigaban kasa to ya cigaba dasu ya kammala kafin ya kafa nashi.. Da haka kasa zata cigaba.

Abubakar Dan Usman yace ana bukatar cigaba da ayyukan tsohuwar gwamnatin da ta gabata. Yayi misali da gina gidan gwaamnati da tsohuwar gwamnatin jihar Neja ta fara amma bata gama ba. Kamata ya yi gwamnatin yanzu ta kammala aikin.

Tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Kebbi Alhaji Abdullahi Lamba Yawuri yace gwamnatin Muhammad Buhari ta fara aiwatar da wasu ayyukan kwarai da tsoffin gwamnatocin baya suka kirkiro amma suka kasa yinsu.

Ga rahoton Nasiru Mustapha Batsari da karn bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG