Binciken ya nuna cewa yawancin yaran sukan bi bola ko kwararo kwararo suna neman kayan bola da zasu sayar su samu kudi kamar yadda aka gani a Yola babban birnin jihar Adamawa.
Wani yaro Aminu da aka sameshi cikin bola ya ce yana neman abubuwan da zai nika ya kai a auna kilo kilo a biyashi, Shi ma wani mai suna Habu da aka sameshi a bola abun da ya keyi ke nan.
To sai dai a jihar ta Adamawa a kokarin dakile matsalar gwamnatin jihar ta hada hannu da ofishin cimma muradun karni na MDG ta kirkiro wani sabon shirin zaburar da iyaye ta hanyar ba iyayen tallafi domin kai yara makaranta. Alhaji Ahmed Lawal dake ba gwamnan jihar shawara ta fuskar cimma muradun karni ya jaddada muhimmancin sabon shirin. Ya ce suna kokarin rage talauci. Ya ce suna biyan mutane nera dubu biyar biyar kan wannan sabon shirin. Gwamnati na bada dubu biyar domin a zagewa mutane talauci su kuma kai yaransu makaranta.
Idan gwamnati ta gano cewa iyayen basa kai 'ya'yansu makaranta za'a dakatar da bada dubu biyar din.
Kamar yadda UNESCO ta fitar kimanin yara miliyan goma ne basa zuwa makarantun firamare a Najeriya.Matsalar ta shafi duk jihohin kasar ne har da Abuja. Sabili da haka ne ma'akatar harkokin mata da yara a jihar Adamawa ta ce ba zata kyale yadda ake sake yara kamar dabbobi suna ta garamba akan tituna. Kwamishanar ma'aikatar Halima Mohammed Hayatu ta bayyana matakan da suke dauka. Suna yiwa iyaye gargadi cewa yara bai kamata suna yawo ba. Yakamata suna makaranta. A jihar makarantar firamare da takardu duk kyauta ne. Haka ma rigunan zuwa makaranta, duk kyauta gwamnati ke bayarwa. Idan gwamnati ta ga yaran suna yawo basu je makaranta ba sai ta kwashesu ta kaisu gidan yara su zama yaran gwamnati gaba daya.
Kawo yanzu inji UNESCO akwai yara kimanin miliyan 57 a duk fadin duniya da basa makaranta kuma akasarinsu suna nahiyar Afirka ne.
Ga karin bayani.