Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Da Birtaniya Sun Sa Hannu A Yarjejeniyar Cinikayya Da Harkokin Tsaro


Theresa May da Muhammadu Buhari
Theresa May da Muhammadu Buhari

Firai ministar Birtaniya ta isa Abuja babban birnin kasar Najeriya yau Laraba a kwana na biyu na ziyarar kasashen Afrika ta farko da take yi tun hawanta karagar mulki, a daidai lokacin da Birtaniya ta fice daga Kungiyar Tarayyar Turai.

Yayin ziyarar ta Theresa May a Abuja bayan tattaunawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, sun sa hannu a yarjejeniyar harkokin tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki.

A cikin hirarshi da manema labarai bayan ganawar, ministar harkokin kasashen ketare na Najeriya Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa, shugabannin biyu sun kulla yarjejeniya a wadannan fannonin biyu ne da suka dauka da matukar muhimmanci. Yace yarjejeniyar tsaron da aka kulla zata taimaki Najeriya ta tunkari kalubalar tsaro da take fusakanta , da suka hada da horas da rundunonin tsaro da kuma kare hakkin bil’adama.

Dangane kuma da bunkasa tattalin arziki, yace, kasashen biyu zasu duba hanyoyin da zasu marawa juna baya su kuma amfana daga dangantakar. Yace kasancewar birnin London cibiyar harkokin kudi, da kuma tarin guraban zuba jari dake Najeriya, kasashen biyu zasu samar da dama ga kamfanoni masu zaman kansu da kuma gwamnati.

Dangane da Zabe

Yayin jawabinsa a ganawar da Theresa May, shugaba Muhammadu Buhari ya bada tabbacin gudanar da zabe mai sahihanci a shekara ta dubu biyu da goma sha tara.

Shugaba Buhari yace, ‘‘Ina baki tabbacin cewa, a shirye nake in gudanar da zabe mai sahihanci. Ina farin cikin ganin jam’iyata na kokari sosai. Nasarorin baya bayan nan da aka samu a zabukan jihohin Katsina, Bauchi, da Kogi sun kara mana kwarin guiwa ainun. Nigeria ta rungumi tsarin damokaradiya mai jam’iyu da dama, saboda haka wannan yana sa ‘yan siyasa su kara azama.”

Cin Hanci da Rashawa

Dangane da yaki da cin hanci da rashawa kuma. Shugaba Muhammadu Bujari ya yaba goyon bayan da Najeriya ke samu daga Birtaniya, yace nasarar yaki da cin hanci da rashawa tana da muhimmanci kwarai ga ‘yan Najeriya.

Ficewar Birtaniya Daga Tarayyar Turai

Dangane kuma da ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai shugaba Buhari yace, wannan ya bada damar kara dankon zumunci na tarihi dake tsakanin Najeiya da kasar Turai.

Yace ‘‘Muna kallon abinda ke faruwa game da ficewar daga kungiyar tarayyar Turai a tsorace, sabili da mun sani wannan dangantaka ce da aka dade da kullawa. Na hakikanta cewa, ke da ni a shirye muke mu kara dankon dangantakar dake tsakanin kasashenmu .’’

Shugaba Buhari ya kuma godewa Birtaniya sabili da goyon bayanta a fannin harkokin tsaro da yaki da tashin hankali a Arewa maso gabashin Najeriya, da kuma inganta dangantakar cinikayya tsakanin kasashen biyu ‘‘

Jawabin Theresa May

A nata jwabin, Firai Minista Theresa May, tayi na’am da tabbacin da gwamnatin Najeriya ta bayar na gudanar da zabe mai sahihanci a shekara ta 2019, tace, tana farin cikin zuwa Abuja domin ci gaba da tattaunawar da suka fara da Shugaba Buhari a London cikin watan Afrilu na wannan shekarar, musamman a fannin harkokin tsaro da cinikayya da dawo da kaddarori da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Theresa May tace, “hadin kai a fannin harkokin tsaro yana da muhimmancin gaske a yunkurin shawo kan kungiyar Boko Haram da kuma kungiyar IS a Afrika ta yamma.”

Dangane kuma da maido da kaddarorin Najeriya, Firai Ministar ta shaidawa shugaba Buhari cewa, “bamu so mu rike wani abu da yake mallakar al’ummar Najeriya, sai dai muna bin abinda doka ta shinfida, wadda take daukar lokaci’’

Firai ministar ta kuma yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da matsayin na shugaban kungiyar ECOWAS wajen shawo kan matsalar safarar bil’adama a yankin.

Theresa May ta fara ziyarar kasashe nahiyar Afrika ne ranar Talata a Cape Town inda tayi alkawarin bada fifiko kan Afrika a fannin zuba jari.

Daga Najeriya Firai Ministar zata kuma kai ziyara kasar Kenya a jerin ziyarar kasashen Afrika da Birtaniya ke yi biyo bayana ficewarta daga kungiyar Tarayyar Turai .

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG