Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Da Croatia: Wa Zai Fara Da Kafar Dama?


'Yan wasan Najeriya suna atisaye
'Yan wasan Najeriya suna atisaye

Najeriya da Croatia da ke rukunin "D" za su kara a wasanninsu na farko a ci gaba da gasar cin kofin duniya da ake yi a Rasha wacce aka fara a wannan mako.

Ya zuwa yanzu, kasashen Afirka biyu sun buga wasanninsu a ci gaba da gasar neman cin kofin duniya da aka fara a kasar Rasha a juko na 21, kuma dukkaninsu ba su kai labari ba.

Masar ta sha kashi a hannun Uruguay da ci 1-0, Morocco kuma ta zirawa kanta kwallo a ragarta, lamarin da ya bai wa Iran nasara da ci 1-0.

Wasannin tashin farko, ko kuma "Group Stages" a turance, na da matukar muhimmacin a kowacce irin gasa, su suke daidaita tafiyar kowacce kungiyar kwallon kafa.

A wannan mataki, nasara (win) ita aka fi tururuwar nema kuma abin so, yin kunnen doki (draw), ya fi babu, sannan faduwa (lose) a wasan, shi ne mataki na karshe da babu wanda ke kauna.

Najeriya, ita ce kasa ta uku daga nahiyar Afirka da za ta fara buga wasanta a yau Asabar a rukunin "D", inda za ta kece raini da Croatia a filin wasan Kaliningrad.

TAURARIN 'YAN WASAN NAJERIYA

Kelechi Iheanacho: Ko da yake akwai kwararrun 'yan wasa a tawagar ta Najeriya irinsu, Mikel Obi da Victor Moses, wani dan wasa da zai fi haskakawa a cewar jaridar wasannin ta yanar gizo ta Mirrow shi ne dan wasan gaba Kelechi Iheanacho na kungiyar Leicester City ta Ingila.

Mai shekaru 21 kacal, Iheanacho ya zira kwallaye 13 ma Super Eagles, ana kuma ganin zai taka muhimmiyar rawa a wasannin da kungiyar za ta buga a wannan gasa.

Alex Iwobi: baya ga, Iheanacho, wani dan wasa da ake ganin zai nuna bajintarsa a tawagar ta Super Eagles , shi ne Alex Iwobi (Arsenal) wanda ya gaji yawancin dabarun buga kwallon kawunsa Jay Jay Okocha.

Ahmed Musa: Sannan sai Ahmed Musa, (Leicester City- aro zuwa - CSKA Moscow) wanda ya lakanci sirrin zira kwallaye. Ya kasance dan wasan gaba mai kuzari, wanda ya iya cin kwallaye na ba-da-mamaki.

TAURARIN 'YAN WASAN CROATIA

Luka Modric: A bangaren 'yan wasan Croatia, dan wasan da za a fi sa wa ido shi ne Luka Modric, wanda ke bugawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

"Modric ba dan wasa ne mai gudun gaske ba, amma kakkarfa ne wanda ke amfani da jikinsa wajen lailaya kwallo yadda yake so." Inji shafin yanar gizon dandalin wasanni na CBSsports.com.

Sai dai wasu masu sharhi suna ganin shekarunsa wadanda suka kai 32 sun fara ja.

Domagoj Vida: Dan shekaru 29, Vida mai tsaron gida ne wanda ba ya nuna fargabarsa a filin wasa, yana kuma daya daga cikin dodannin tawagar 'yan wasan na Croatia.

Wasu suna mai kallon mutum ne mai yawan farfar, wanda hakan ya sha janyo mai jan kati a wasannin, amma dai an yi ittifakin cewa zai taka rawar gani kwarai a gasar ta 2018.

SHIN NAJERIYA TA TABA HADUWA DA CROATIA?

Ba kamar Argentina ba, wacce ita ma ta ke rukunin na "D", Croatia ba ta da tarihin karawa da Najeriya a fagen wasan kwallon kafa, hakan ya sa masu sharhi ke wahalar yin fashin baki kan yadda karawar za ta kaya.

Amma watakila a iya samun 'yar mahanga daga tarihin yadda kasashen biyu suka taka leda a wasannin gasar ta cin kofin duniya da aka yi a baya.

RAWAR DA NAJERIYA TA TAKA A GASAR CIN KOFIN DUNIYA TA USA 94

Kusan daukacin masharhanta a fagen wasan kwallon kafa sun yi ittifakin cewa, gasar cin kofin duniya da aka yi a Amurka a 1994 wanda shi ne lokaci na farko da Najeriya ta je, ta kasance gasar da ta fi nuna rawar gani cikin tarihinta na zuwa gasar.

A wannan lokaci, tauraruwar Najeriya na kan haskawa, domin ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka kenan, inda har kasar ta kai matakin kasa ta 5 da ta fi iya taka leda a duniya a kiyasin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

A zangon farko, ko kuma group stages, Najeriya ta ci wasanninta biyu, kafin ta hadu da Argentina, wacce ta nuna mata kwarewa ta doke ta.

Daga baya kuma ta hadu da Italiya, wacce ta fitar da ita daga gasar.

RAWAR DA CROATIA TA TAKA A GASAR CIN KOFIN DUNIYA TA FRANCE 98

Ita kuwa Croatia, a France 98 ne ta yi fita mai kyau, inda tun daga wannan lokaci, tauraruwarta ta daina haskawa a gasar cin kofin duniya.

Har ta kai ga ta samu kyautar tagulla (bronze) bayan da ta zo ta uku a karshen gasar.

Kamar na Najeriya, 'yan wasan na Croatia, sun ba da mamaki matuka, lura da cewa gasar ta France 98, ita ce fitarsu ta farko.

Baya ga haka dan wasanta Davor Suker, wanda ya jagoranci tawagar, shi ya lashe kyautar dan wasan da ya fi zira kwallaye (6) a gasar.

ABIN TUNKAHO GA KASASHEN BIYU

Yayin da kasashen biyu suke shirin karawa a yau Asabar, baya ga wasu batutuwa na daban, abin da ya fito karara shi ne, kowanne bangare na tunkaho da abu guda.

A bangaren Najeriya, duk nasarorin da ta taba samu a tarihin gasar cin kofin duniya, akan kasashen nahiyar turai ne, ta kara da kasashe 11, ta yi nasara a wasannin biyar an lallasa ta a wasannin biyar ta kuma yi kunnen doki a wasa guda.

Najeriya ta doke Bulgaria 3-0 a zuwanta gasar a karon farko a USA 94, sannan ta lallasa Spain da ci 3-2 a France 98.

Ita kuwa Croatia, a zuwanta gasar na farko ta kai matakin samun tagulla (bronze) bayan da ta zo ta uku a gasar cin kofin duniya da aka yi na France 98.

Arwar wannan tarihi da ta kafa tun a wancan shekaru na ci gaba da yin tasiri a yanayin wasan tawagar kwallon kafar kasar har yanzu kamar yadda jaridar yanar gizo ta Croatiaweek.com ta wallafa.

Yanzu wa zai nuna daya cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne a tsakanin bangarorin biyu?

Lokaci ne kawai zai nuna a karawar da za a yi a filin Kalingrad da ke Rasha.


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG