Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya da UNESCO Suna Kokarin Kawar Da Cin Zarafin Mata A Makarantu


UN
UN

Gwamnatin tarayyar Najeriya tare da hadin gwuiwar Cibiyar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin Ilimi, kimiyya da al’adu UNESCO, da sauran masu ruwa da tsaki sun fara tattaunawa domin samun mafita mai dorewa a game da matsalar cin zarafin mata a a makarantu a fadin kasar.

Tuni aka kafa wani kwamitin da zai yi duba na tsanaki a fannin shari’a domin tabbatar da an hukunta masu aikata wannan aika-aika na cin zarafin yara mata a makarantu a Najeriya.

A jawabin da ta gabatar a wurin bukin kaddamar da kwamitin a ranar Litinin a Abuja, babbar lauyar tarayyar Najeriya kuma babbar sakatariyar ma’aikatar shari’a ta Najeriya Mrs. Beatrice Jedy-Agba, ta bayyana cewa, yara suna da hakkin a kare su daga duk wani nau’in tashin hankali, a gida ko a makaranta.

A bisa wannan dalili ne ya sa ta bukaci gwamnatin da samar da kundin tsarin aikin da zai yi wa masu ruwa da tsaki a makarantu a fadin Najeriya domin fuskantar duk wani batun cin zarafin da zai iya tasowa.

Jeddy-Abga ta bayyana cewa, kwamitin ida aka kafa akan matsalaolin cin zarafin matan a makarantu zasu yi aiki tare da sashin dake kula da al’amuran da suka shafi cin zarafi domin aiki tare wajen samar da kundin da zai bada bayanan mataken da za a dauka idan aka samu aukuwar irin wadannan matsaloli na cin zarafin a makarantu.

Ta kuma yi kira ga mambobin kwamitin da aka zakulo su daga ma’aikatun gwamnati daban daban su dauki wannan aiki da mahimmanci domin tabbatarwa yaran Najeriya da kariya a makarantu.

Shima Mr. Stephen Onyekwelu wanda ya wakilci kungiyar UNESCO ya ce babu yadda za a kawar da matsalar cin zarafi ba tare da illimi ba.

Ya bayyana cewa, ”Illimi yana da mahimmanci wajen sauya wasu halayya, da dabi’u kuma muna iya daukan matakai domin ganin cewa starin ilimin mu ya magance matsalolin cin zarafin mata a fadin duniya”

Muna aiki tare da ma’aikatar illimi ta tarayyar da a halin yanzu muna sake duba tsarin dokokin makarantun sakandari wanda za a gabatar a majalisar kolin Ilimi ta kasa wadda za a yi nan ba da jimawa ba

XS
SM
MD
LG