Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Magidanta Na Korafi Kan Tsadar Kayan Masarufi


Masu sayar da tumatir a kasuwar Mile 12 da ke Jihar Legas a kudancin Najeriya
Masu sayar da tumatir a kasuwar Mile 12 da ke Jihar Legas a kudancin Najeriya

Yayin da ake cigaba da azumtar watan Ramadana a duk fadin duniya, a Najeriya magidanta na korafi kan yadda ake samun hauhawan farashin kayan masarufi.

A watan na Ramadana, akan zargi ‘yan kasuwa da kara farashin kayayyakin abinci saboda yawan bukatar su da ake yi.

Sai dai malamai su kan yi wa’azin kira ga ‘yan kasuwar da su daina yin hakan musamman a watan na Ramadana, lura da cewa wata ne na neman lada.

Amma ‘yan kasuwar su kan musanta wannan zargi da ake musu na kara farashin kayan masarufi.

Jihar Naija da ke tsakiyar Najeriya, ita ma ta na fama da irin wannan matsala ta hauhawan farashin kayayyakin abinci a watan na azumi.

Saurari wakilin Muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari da wannan rahoto da ya aiko daga Minna kan tashin farashin kayan masarufi yayin da azumin na watan Ramadana ya kai shida:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG