Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Masu Coronavirus Sun Haura Dubu Daya


Wasu ma'aikatan lafiya biyu suna karawa juna karin gwiwa yayin da suka fagen fama a yaki da Cutar coronavirus a Amurka

Cikin sa’a 24, Najeriya ta samu karin mutum 114 da suka kamu da COVID-19, kwayar cutar da ke haddasa coronavirus, a cewar hukumar kare yaduwar cututtuka ta NCDC a kasar.

Jihar Legas da ke kudu maso yammacin kasar, ta samu karin mutum 80 a rana daya, sai Gombe 21, Abuja biyar yayin da Zamfara ta samu mutum biyu.

Sauran yankunan da aka samu karin masu dauke da cutar a cewar NCDC sun hada da jihar Edo mai mutum biyu sannan Ogun, Oyo, Kaduna da Sokoto duk sun samu karin mutum dai-dai.

“Ya zuwa karfe 11:30 na dare (agogon Najeriya) ranar 24 ga watan Afrilu, mutum 1095 aka tabbatar suna dauke da cutar #COVID19 a Najeriya.” NCDC ta bayyana a shafinta na Twitter @NCDCgov.

Shafin ya kara da cewa ya zuwa yanzu mutum 32 suka mutu a kasar sannan an sallami 208.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG