Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Mutane Suka Fi Bacewa A Duniya


A Najeriya Kungiyar Bada Agaji ta Duniya ta ce mutane dubu 22 sunyi batan dabo a shiyar Arewa Maso Gabashin Najeriya.

Shugaban Kungiyar Peter Muarer ne ya baiyana haka a lokacin da ya ke ganawa ta musamman da manema labarai a Abuja, inda yayi bukin cika shekaru 70 da kafa Kungiyar.

Peter Muarer yace wannan alkaluma shi ne alkaluma mafi girma da aka taba samu na mutanen da suka bace a duk duniya.

Peter yace Kashi 60 na wadanda suka bace din yara ne, wanda hakan ke nuna dubban iyaye ba su san inda yaran su suke ba, ko kuma halinda suke ciki ba, ko suna da rai ko babu rai.

Muarer ya kara da cewa sun hada hannu da jami'an kasa da kasa domin su yi aiyukan su yadda ya kamata, kuma a bisa dokokin kare hakki, da kuma lafiyar talakawa yadda doka ta tanada, kuma yace suna lura da take taken juna.

Peter ya kara cewa duk wasu iyaye na kirki tashin hankalinsu shi ne rashin sanin inda 'ya'yansu suke. Wannan shi ne halin da iyaye suke ciki a Najeriya, an barsu kullum suna cikin kokarin nemo 'ya'yansu. Yace amma sun samu sun gano mutane 367 da kyar daga shekara 2013 zuwa yanzu.

A lokacin da yake nazarin aiyukan Kungiyar Farfesa Mohammed Taofik Ladan na Cibiyar koyar da Demokradiyya ta Majalisar Dokokin Najeriya, yace ana horad da sojojin Najeriya jefi jefi domin su kare talakawaa lokacin yaki, ko tashin tashina da kesa mutane cikin halin ha'ula'i. Saboda haka suna kokarin bin dokkokin Kasa da Kasa alokacin yakin Boko Haram.

Rahoton yace an raba masoyi da masoyi,an kashe yara kanana, a harin bomabomai kuma an lalata gidaje. Iyalai ne wadanda suka fi ta6uwa a sakamakon rikicin Boko Haram, da aka kwashe shekara 10 ana bugawa.

Ga cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00Facebook Forum

XS
SM
MD
LG