Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya na Daukan Matakan Dakile Fatauchin Miyagun Kwayoyi


Miyagun kwayoyi.

Hukumomin Nigeria na nuna matukar damuwar ganin yadda amfani da miyagun kwayoyi yanzu ke yiwa jihar Borno babbar barazana.

Jami’an tsaro a Nigeria sun bayyana cewar sun kwace damin haramtacciyar kwaya da nauyinta ya haura ajin nauyin waya (Ton) shida, da suka hada da hodar Iblis ta (Cocaine) da (Marijuana) a yankunan Arewa maso gabashin jihar Borno a wannan shekarar. Jami’an hukuma na matukar nuna damuwar ganin yadda safarar kwaya da yin amfani da kwayar ke kara habaka a yankunan da har ta kai matsalar na yin barazana ga yankunan, duk da ci gaba da daukan kwararan matakan tauye gwiwar da jami’an tsaro ke yiwa masu tsatsauran ra’ayin Islama.

Bugu da kari kuma, banda samun nasarar kame tulin damin kwayar da jami’an keyi ana kuma tsare da mutane sama da 61 a watanni shidan da suka gabata, kamar yadda jami’an tsaro na musamman ke bayyanawa. Jami’an hukuma sun nunawa taron manema labarai wasu dakuna biyu dake ciki makil da damin kwayar da suka kama da kudinta aka kiyasta ya kai Dolar Amurka miliyoyi masu tarin yawa.
XS
SM
MD
LG