Wani rahoto da bankin raya kasashen Afrika ya fitar ya yi nuni da cewa Najeriya na amfani da kashi 50 cikin 100 na kudaden shigarta wajen biyan kudin ruwan basussuka da ta karbo daga kasashen ketare.
Wannan rahoto na zuwa ne, a daidai lokacin da hukumomin Najeriya ke cewa suna shirin kara ciwo basussuka domin gudanar da wasu ayyuka.
A cewar Malam Yusha’u Aliyu, masani kan harkokin tattalin arziki, ba illa ba ne idan Najeriya ta karbo bashi, amma dai abu mai matukar muhimanci ne da ya kamata mahukunta su mai da hankali akan shi.
“Gaskiya abin damuwa ne a ce kasar da take da albarkatun mai take da yawan jama’a, a ce kuma irin wannan kaso yana tafiya wajen biyan kudin bashi.”
Amma a cewar, Yusha’u, shi bashi ba matsala ba ne a karbe shi, “matsalar ita ce yanayin irin kudin ruwan da za a biya akan bashin.”
Saurari cikakken hirar Malam Yusha’au Aliyu da Mahmud Lalo.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 03, 2023
'Yan Kasashen Waje Masu Saka Ido A Zabe Sun Fara Isowa Najeriya
-
Fabrairu 03, 2023
Kotu Ta Raba Auren Diyar Ganduje
-
Fabrairu 03, 2023
Wani Bene Mai Hawa Uku Ya Rushe a Abuja
-
Fabrairu 02, 2023
Al'ummar Najeriya Sun Shigar Da Karar Kamfanin Shell A Kotu A Landan
Facebook Forum