Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Shirin Kashe Dala Miliyan 10 a Yankin Niger Delta


Tsagerun yankin Niger Delta.
Tsagerun yankin Niger Delta.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta saka tallafin Dala Biliyan 10 a yankin Niger Delta, da nufin kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga da kuma raya yankin.

Karamin Ministan albarkatun man fetur da ma’adinai, Emmanuel Ibe Kachikwu, shi ne ya bayyana kudurin gwamnatin Najeriya na kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin Niger Delta, da kuma farfado da yankin mai arzikin albarkatun man fetur.

Sai dai masana harkokin tattalin arziki na ganin wannan mataki da gwamnatin Najeriya ke shirin dauka tamkar koma baya ne dangane da matakin da take shirin dauka na ba sani ba sabo akan tsagerun yankin masu lalata albarkatun mai ta hanyar kai hare-hare.

Dakta Dauda Muhammed Kontagora, masanin tattalin arziki da saka jari a jami’ar Bayero dake Kano, ya ce abin tambaya anan shine a can baya an kashe kudade ta hanyar gudanar da wasu shirye-shirye domin tallafawa mazauna yankin, amma ba su dai na barnar da suke yi a yankin ba, saboda haka tabbas wannan shiri da gwamnati za ta sake kaiwa yankin ba lalle bane ya yi tasiri.

Tun daga shekarar 2010 zuwa 2012 Najeriya ta sami Dala Tiriliyan 1.5 daga cinikin man fetur da take hakowa a yankin Niger Delta, lamarin da al’ummar yankin ke ganin ya kamata su ma a kara musu kason da suke samu.

Sai dai kuma hare-haren da ‘yan bindigar suka fara kaiwa tun bayan hawan mulkin shugaba Buhari, na mayar da hannun agogo baya.

Lamarin da ya sa gwamnati ta mayar da hankali a bangaren noma da hanyoyin sadarwa da yawon bude ido da kuma hakar ma’adanai.

Domin karin bayani saurari rahotan Babbangida Jibrin.

XS
SM
MD
LG