Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Shari'ar Shugaban Masu Gwagwarmayar Neman 'Yancin Biafra


Prince Ozo Onna ya shiga zanga zangar da akeyi kan shugaban Biafra Nnamdi Kanu.
Prince Ozo Onna ya shiga zanga zangar da akeyi kan shugaban Biafra Nnamdi Kanu.

A Najeriya, za a koma zaman shari’ar shugaban masu gwagwarmayar neman aware na Biafra yau Talata, amma mai shari’ar da ke kula da karar ta bada umurnin a ci gaba da zaman a sirrance, abin da ya ke kara janyo cece-kuce a cewa Chima Nwanko daga birnin tarayya Abuja.

A lokacin da ‘yan sanda suka kama Nnamdi Kanu a sirrance a birnin Lagos cikin watan Oktoan shekarar 2015, babu wanda ya yi tunanin cewa za a kawo yanzu akan wannan batun. An taba bashi beli sau daya, aka kuma sake kama shi tun daga nan yake tsare, duk da umurini da kotu ta ba da na a sake shi.


A yanzu kuma zancen ya sake canza zane.


A cikin watan Disambar shekarar da ta gabata, mai shari’a Binta Nyako ta rubuta takardar bukatar a yi shari’ar Kanu a sirrance. Canje-canjen da aka samu akan shugaban na ‘yan Biafra sun hada da laifuffukan zagon kasa da cin amanar kasa.


Zanga-zanga a kudu maso gabashin kasar dangane da kamen Kanu sun haddasa kisan mutane da yawa, a cewar kungiyoyin rajin kasar.
Kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fada a cikin wata Nuwamban bara cewa sojojin kasar sun so su wargaza wannan yinkurin, sakamakon haka mutane 150 masu goyon Biafra suka mutu tun daga watan Agustan shekarar 2015. ‘Yan sanda da jami’an tsaro sun yi watsi da wannan zargin, sai dai ma suka zargi masu zanga-zangar da ta da kayar baya.

XS
SM
MD
LG