Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Cika Shekaru 56,Ta Tsallake Rijiya Sau Da Yawa-Maitama Sule.


Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa PM Najeriya na farko.

Tun a lokacin gwagwarmayar neman 'yancin kai kasar take fadawa rigingimu amma sai ta fito daram-Inji Maitama Sule Dan Masanin Kano.

Daya daga cikin dattijan Najeriya tun jamhuriya ta farko Alhaji Maitama Sule, ya jinjinawa Najeriya saboda irin fitintinu da kasar ta fada tun zamanin lokacin neman 'yancin kai, amma Allah cikin ikonsa sai kasar ta mike.

Dan masanin kanon yace, rigingimun sun hada harda zaben 1959 lokacinda aka kasa samun jam'iyya daya wacce zata iya kafa gwamnati, saboda haka ya zama tilas a kafa gwamnatin kawance, shima sai da aka kusa kai ruwa rana.

Alhajai Maitama Sule, ya kuma tabo batun zaben 1964, wanda shine ya kai ga wasu suke ganin dalilin da ya jefa kasar cikin yakin basasa.

Ga karin bayani.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:05:13 0:00

XS
SM
MD
LG