Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Doke Ethiopia a Calabar


'Yan wasan Super Eagles sun doke takwarorinsu na kasar Ethiopia da ci 2-0 a karo na biyu na neman wacece zata haye zuwa Brazil a tsakaninsu

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya sun samu hayewa zuwa ga gasar cin kofin kwallon kafar duniya da za a yi a kasar Brazil a shekara mai zuwa.

Wannan ya faru ne a bayan da suka doke 'yan wasan kasar Ethiopia a zagaye na biyu na karawar da kasashen biyu suka yi domin zaben dayarsu da zata shiga cikin wakilan Afirka a wannan gasa ta duniya.

A karawar farko da aka yi cikin watan da ya shige a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia ma, 'yan wasan na Super Eagles ne suka samu nasara da ci 2-1. Wannan na nufin cewa Najeriya ta lashe wannan karawa tsakaninsu da ci 4-1.
XS
SM
MD
LG