Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Gindaya Sharuddan Sassauta Dokar Zirga-zirga


Hoton sanarwar sharuddan da aka gindaya wa mutane a Najeriyar
Hoton sanarwar sharuddan da aka gindaya wa mutane a Najeriyar

Daga ranar 4 ga watan Mayu ne za a sassauta dokar da ta takaita zirga-zirga a birnin Abuja da kuma jihohin Legas da Ogun na Najeriya.​

Sai dai gwamnati ta gindaya wasu sabbin ka'idoji wadanda za su zamanto tilas mutane su kiyaye su idan aka fara fita.

A cewar wata sanarwar da mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmed ya fitar, wadannan sharuddan da aka gindaya domin rage yaduwar cutar Coronavirus zasu fara aiki ne a yau Litinin.

Sanarwar ta ce dole ne a samar da takunkumin rufe fuska da sinadarin kashe kwayoyin cuta da na wanke hannu, da kuma cibiyoyin gwada yanayin zafin jikin mutane a duk wurin da aka san za a rinka yawan taruwa.

Ta kuma tilasta wa mutane barin tazara na akalla mita 2 a tsakaninsu, da hana shagulgulan wasanni.

A cewar sanarwar, har yanzu dai wuraren ibada, da makarantu da kuma gidajen rawa da shakatawa za su ci gaba da zama a garkame.

A cikin wuraren da za a bude, akwai bankuna da ofisoshi masu zaman kansu da na gwamnati da kuma kasuwanni.

Amma wadannan wuraren za su kasance a bude ne daga karfe 8 na safe zuwa 2 na rana.

Kasuwannin unguwa kuwa, za a bude su ne so uku a mako daga karfe 8 zuwa karfe 3 na rana.

Yayin jawabi da ya yi wa 'yan kasar a makon da ya gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin sassauta wannan dokar ta zama a gida wacce ta yi akalla wata daya tana aiki.

An gindaya wadannan dokokin ne domin ci gaba da tabbatar da takaita yaduwar cutar coronavirus wacce a yanzu ta harbi mutum 2,558 a Najeriyar.

Cutar ta kuma kashe mutum 87 a kasar, yayin da wasu 400 suka samu waraka.​

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG