Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jan Kunnen 'Yan Kasuwa Akan Shiga Najeriya Da Kayan Jabu


Shugaba Muhanmadu Buhari

Shugaba Muhammad Buhari ya fada a birnin New Delhi cewa duk da faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya gwamnatinsa ta dukufa wajen tabbatar da daidaita tattalin arzikin Najeriya da nufin karfafawa masu saka jari guiwa.

Yayinda yake tattaunawa da shugabannin manyan masana'antun kasar Indiya da suke da jari a Najeriya shugaba Buhari yace yana da karfin gwuiwar cewa idan aka yi la'akari da irin kwararrun mutane da kasar take dasu da albarkatun da Allah ya bata bai makata faduwar farashen mai ya shafeta ba ainun.

Yace abun da yakamata kasar ta yi wanda kuma gwamnatinsa ta dukufa da yin hakan shi ne dakile kashe kudi akan banza da wofi tare da hana almubazaranci. Yace dalili ke an da gwamnatinsa ta fito da shirin samun asusu daya na gwamnati. Yin hakan zai hana kashe kudi barkatai da aka saba yi da can..

Shugaba Buhari yace ya san daukan irin wadannan matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da hana yin watanda da kudaden jama'a ka iya shafar harkokin kasuwanci amma na wani dan takaitacen lokaci saboda matakai ne da suka dace a dauka.

Ganin cewa akwai dangantakar abokantaka ta kwarai tsakanin Indiya da Najeriya shugaba Buhari yace ya kamata kasashen su kara fadada harkokin kasuwanci su wuce dalar Amurka biliyan 16.36 da suke yanzu. Akwai fannoni kaman noma da fasaha da makamashi da hanyoyin sadarwa da ilimi da dai makamantansu da kasashen zasu iya fadada kasuwancinsu inji Shugaba Buhari..

Daga karshe shugaba Buhari ya ja kunnuwan 'yan kasuwan cewa kasarsa ba zata amince da shigowa da kayan jabu ba daga Indiya.

XS
SM
MD
LG