Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Janye Jakandanta A Indonesia Bayan Cin Zarafin Da Aka Yi wa Jami'inta


Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama (Facebook/ Ma'aikatar harkokin hajen Najeriya)
Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama (Facebook/ Ma'aikatar harkokin hajen Najeriya)

Ministan al’amuran kasashen wajen Najeriya Geofferey Onyeama, ya ce gwamnatin Najeriya ta bukaci hukumomi a Indonesia su dau mataken ladabtarwa akan jami’anta da suka ci zarafin jami’inta na diflomasiyya a Jakarta.

Ministan ya ba da wannan sanarwar a wata zantawa da yayi da ‘yan Jarida jim kadan bayan ganawa da jakadan kasar Indonesiya Usra Harahap da zimmar bayyana masa rashin jin dadin gwamnatin Najeriya game da faruwar wannan al’amari.

Wani hoton bidiyo ya karade kafafen sadarwa na zamani, da ke nuna wasu jami’an shige-da-ficcen Indoneasiya uku yayin da suke cin zarafin wani jami’in diflomasiyyar Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa tuni hukumomin kasar suka janye ambasadan Najeriya a Indoneasiya Usman Ogah, domin tattaunawa da shi ciki har da batun sake duba akan mu’amala tsakanin kasashen biyu.

Ministan ya bayyana cewa ma’aikatar ta tuntubi jakadan bayan ganin yadda aka makure jami’in a wuya cikin wata mota da ke tafiya, domin tabbatar da abin da idanuwan su suka gane musu, inda kuma ya tabbatar musu cewar lallai abin da suka gani a bidiyon ya faru kana ya zayyana wa ma’aikatar yadda al’amarin ya auku.

Ya kara da cewar ambasasadan ya ce wannan mumunan aikin ya auku ne a lokacin wani zagayen da jami’an shige-da-ficcen Indonesiyan suka yi domin neman bakin hauren da suka shigo kasar ba da cikkaken izini ba.

Oyeama ya sanar cewa abu na farko da ma’aikatar ta yi shine ta bukaci ambassadan Najeriya a kasar ta Indoneasia ya ba da cikkaken rahoto kan lamarin a rubuce, sannan daga bisani ta umarce shi da ya shigar da karar aukuwar wannan al’amari a ma’aikatar kasashen wajen Indonesiya.

Ministan ya bayyana al’amarin da cewa ya sabawa yarjejeniyyar Vienna.

"Bayan da muka yi nazarin rahoton Ogah, mun sake jaddada matsayar mu akan wannan al’amari cewa babu wata hujja da ta bada damar a aikata irin abun da jami’an suka aikata" in ji Onyeama.

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG