Accessibility links

Najeriya ta Lashi Takobin Kawar da Polio Nan da 2015

  • Garba Suleiman

Wasu nakasassu a Kano.

Hukumar Kiwon lafiya Tun Daga Tushe ta Najeriya ta ce ganin yadda aka samu nasarar dakile yaduwar kwayar cutar Polio a 2013, ana iya kawar da cutar baki daya nan da 2015

Hukumar Kiwon Lafiya Daga Tushe ta Najeriya ta ce ganin irin nasarar da aka samu wajen dakile bazuwar jinsin kwayar cutar Polio da ake kira “Wild Polio Virus” ko WPV a takaice, inda aka samu bullarsa sau 50 kawai a shekarar 2013, hukumar ta kuduri aniyar ganin an kawar da kwayar cutar daga Najeriya nan da shekarar 2015.

A lokacin da yake jawabi ga ‘yan jarida a Abuja, sakataren gudanarwa na hukumar, Dr. Ado Mohammed, yace a wannan shekara da zamu fita, an samu raguwar bullar kwayar cutar ta Polio da fiye da kasha hamsin cikin 100, in an kwatanta da shekarar 2012, inda aka samu bullar wannan cuta sau 121 a fadin Najeriya.

Amma kuma, Dr. Ado Mohammed ya roki mata masu juna, musamman a jihohi kamar Borno da Kano da Yobe, da su rika zuwa cibiyoyin kiwon lafiya mafi kusa domin a samu raguwar mace-macen uwaye da jarirai.

Shugaba Goodluck Jonathan dai ya fada a cikin watan Nuwamba cewa gwamnatinsa zata yi bakin kokarinta domin kawar da cutar Polio baki daya daga Najeriya nan da shekarar 2015.
XS
SM
MD
LG