Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Sake Bude Lamurran Wasanni


Najeriya Ta Bude Lamurran Wasanni Bayan Coronavirus
Najeriya Ta Bude Lamurran Wasanni Bayan Coronavirus

Gwamnatin Najeriya ta amince da sake bude lamurran wasannin lig na kwallon kafar kasar, to amma da sharadin ba bu ‘yan kallo a filayen wasa, a wani yunkuri na sassauta dokokin annobar coronavirus.

An dakatar da buga wasannin lig na kasar ne a watan Maris, a yayin da ya rage zagaye 13 na wasannin na lig, sakamakon barkewar annobar ta COVID-19.

Jami’in kwamitin musamman na shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19 Sani Aliyu, ya ce “an dage dokar ne ga wasannin da ake bugawa a budaddun filayen ba tare da cunkoson jama’a ba, da kuma amfani da wuraren motsa jiki da wasannin lig duk za su dawo amma ba tare da ‘yan kallo ba a filayen wasa.”

Najeriya Ta Bude Lamurran Wasanni Bayan Coronavirus
Najeriya Ta Bude Lamurran Wasanni Bayan Coronavirus

An jima ana kiran da a sake dawowa da fafata gasar ta lig ta Najeriya, biyo bayan sassauta dokokin hana zirga-zirga da aka kafa sakamakon annobar ta coronavirus.

To sai dai ba’a bayyana takamaiman lokacin da za’a ci gaba da wasannin ba, amma jami’ai sun ce za’a soma sabuwar kakar wasanni a karshen wannan watan, ko watan Oktoba mai zuwa.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG