Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Sami Koma Baya A Yaki Da Mutuwar Jarirai


Dan jariri
Dan jariri

Wani sabon rahoton da aka buga kan rayuwar kananan yara ya nuna cewa Nigeriya bata sami wani ci gaba ba a daukar maatakan maganin mace macen kananan yara a cikin shekaru goma da suka wuce.

Wani sabon rahoton da aka buga kan rayuwar kananan yara ya nuna cewa Nigeriya bata sami wani ci gaba ba a daukar maatakan maganin mace macen kananan yara a cikin shekaru goma da suka wuce.

Rahoton ya nuna cewa, duk da yake ya rage saura shekara biyu a kai shekara ta 2015, Nigeriya wadda take daya daga cikin kasashe 25 dake da yawan mutuwar yara, bata sami wani ci gaba ba a daukar matakan maganin matsalar wanda ya nuna zai yi wuya kasar ta iya kaiwa ga nasara a cimma muradun karni musammam a fannin rage mutuwar kananan yara.

Rahoton da aka ba sunan Ajandar Kare Mutuwar Yara, ya yi nazarin matakan da kasashen suka dauka cikin shekaru gpma na maganin ci gaban mace macen kananan yara ya lura cewa ba a sami ci gaba sosai ba a Najeriya.

Nigeriya ta zama 24 cikin kasashe 75 da suka samu raguwar mutuwar yara kasa da shekara biyar. Rahoton da aka sanar a Abuja ya nuna Najeriya tana bayan kasashe n AFrika da dama da aka sami raguwar mutuwar mutuwar kananan yara kamar, Ethiopia, Liberia, Tanzania, Nepal, Malawi da Bangladesh. Rahoton ya maida hankali kan kokarin masu bada taimako daga 2000 zuwa 2012, wajen rage mutuwar yara. Rahoton ya lura cewa an sami raguwar mutuwar yara kasa da shekara biyar daga 188 cikin 1,000 zuwa 124 – canjin da ya kai kusan kashi 34, amma har ya zuwa kashi 32 na mutuwar dake faruwa na cikin jarirai ne, yadda rahoto ya bayar.

Da yake Magana lokacin kaddamar da rahoton, mataimakin directa na sashen kula da rayuwar kananan yara a ma’aikatar lafiya ta Abuja, Tinu Taylor,ya lura cewa. Ana ci gaba da samun mace macen kananan yara duk da yake ana iya maganin matsalolin da suke sa mace macen da suka hada da ciwukan da suka shafi haihuwa, da kuma matsalolin kamin haihuwa.

Rahoton ya nuna cewa, yawan yara dake samun magani wajen gudawa da rashin bada mama ya ragu. Rahoton ya kuma lura cewa yaran da aka Haifa cikin talauci suna iya mutuwa kusan sau biyu biyu da rabi cikin dari kamin su cika shekara biyar fiye da wadanda aka haifa cikin arziki.

Haka nan kuma, kusan kashi sittin cikin dari na kananan yaran da aka haifa a kauye suna mutuwa kafin su cika shekaru biyar fiye da yaron da aka haifa a birni, kuma ‘yanmata sunfi kusan mutuwa fiye da maza kamin su kai shekara biyar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG