Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Samu Rigakafin Cutar Sankarau Ta Kananan Yara


Rigakafin Ciwon Sankarau
Rigakafin Ciwon Sankarau

Bayanai na nuni da cewa kimanin mutane fiye 10,000 ne ke kamuwa da cutar sankaura a Najeriya a kowacce shekara, inda fiye da 1,000 yara ne.

Gwamnatin tarayya a Najeriya ta ce ta yi nasarar samun alluran rigakafin cutar sankarau ga kananan yara.

Bayanai na nuni da cewa kimanin mutane fiye 10,000 ne ke kamuwa da cutar sankaura a Najeriya a kowacce shekara, inda fiye da 1,000 yara ne.

A hirarsu da wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji, shugaban hukumar kula da lafiya, matakin farko a jihar Filato, Dakta Livinus Miapkwap, ya ce manufar allurar rigakafin shi ne ta kare yara daga kamuwa da cutar ta sankarau.

Shi ma a na shi bayanin, Sakataran ma’aikatar lafiya ta jihar Filato, Dakta Martins Azzuwut, ya ce Najeriya na daga shiyyar da al’ummarta ke kamuwa da cutar sankarau, don haka ake neman mafita kan cutar.

Ga cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG